Batun tattalin arzikin turai ne zai mamaye taron G8

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Bankia

Batun tabarbarewar tattalin arziki a yankin nahiyar turai ne zai mamaye taron koli na kasashe masu karfin tattalin arziki da ake kira G8, a wannan karshen makon.

Wasu ma dai na hasashen cewa kasar Girka zata fuce daga tsarin kudin bai dayan na Euro ko kuma ma rugujewar kudin na Euro.

Ba bu mamaki yawancin rahotanni da ake yi kan tabarbarewar tattalin arzikin Euro zuwa yanzu anayi ne yawanci kan kudade da tattalin arziki ko kuma gwamnatoci da suka yiwo rancen kudade ko kuma wasu gwamnatocin da suka kashe kudade da dama.

Amma abunda akai karancin magana akai shine watakila siyasar dake ciki baki daya.

Kusan dai kudin bai daya abu ne da ya shafi siyasa wanda yake a matsayin wani ginshikin tattalin arziki wanda yake da doguwar alaka tsakanin Faransa da Jamus don tabbatar da kusanci su a yankin.

Karin bayani