An bude taron kasashen G8

Shugabannin kasashen G8 Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Shugabannin kasashen G8

Shugabannin wadatattun kasashe takwas na G8 da ke taro a Amurka sun yi kira ga kasar Girka da ta ci gaba da kasancewa cikin kasashen da ke amfani da kudin Euro.

Sanarwar bayan taro ta ce abu mafi muhimmanci shi ne inganta tattalin arziki da samar da ayyukan yi.

An dai sha kai da kawo yayin tattaunawar. Da ake tattaunawar an tambayi shugaba Obama yadda take gudana, sai ya ce komi lafiya zuwa yanzu amma dai akwai sauran aiki a gabansu.

Kuma da aka tambaye shi ko sun cimma wata yarjejeniya kan kasashen da ke amfani da kudin Euro? Sai ya ce tukunna da sauran aiki a gabansu.

Karin bayani