Ana gudanar da zaben kansiloli a Bengazi

Birnin Bengazi Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Birnin Bengazi

Mutanen birnin Bengazi suna jefa kuri'a a yau don zabar sabbin kansilolin birnin, wanda shi ne cibiyar boren da ya kai ga hambarar da Kanar Gaddafi daga mulki.

Wannan ne karon farko da mutanen Benghazin suke jefa kuri'a cikin shekaru hamsin, an kuma ayyana yau din a matsayin ranar hutu.

Kamar mutane dubu dari biyu ne suka yi rajisatar jefa kuri'a a zaben, inda 'yan takara fiye da dari hudu ke neman zama kansilolin.

Watan gobe ne za a yi zaben 'yan majalisar kasar ta Libya baki daya.

Karin bayani