An gano bama-bamai a Jos, Najeriya

Birnin Jos Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Birnin Jos

Rundunonin tsaro dake aiki a jihohin Borno da Filato a arewacin Najeriya sun kai samame a wani gida dake Unguwar Rikkos a birnin Jos inda suka ruguza gidan, sannan suka gano muggan makamai ciki har da bama-bamai.

Hukumomin dai sun bayyana cewa sun yi kwana biyu suna bin sawun wani wanda suke zargi da kasancewa dan kungiyar nan ta Jama'atu Ahlil Sunnah Lidda'awati Wal Jihad wadda aka fi sani da suna Boko Haram da ke zaune a gidan, kuma bisa bayanan sirri, suka far wa gidan.

Jami'an tsaro sun ce mutumin da suke bin sawun ya tsere, amma sun samu yara da mata a gidan.

Sun kuma ce sun gano littattafan addinin Kirista da na Musulunci a gidan.

Kakakin rundunar tsaro ta musammam a jihar Pilato, Kyaftin Marcus, ya shaida wa wakilinmu Ishaq Khalid cewa wadanda ake zargin: "sun boye mata shida da yara kimanin 11 a gidan, mun cece su sannan muka ci gaba da aiki."

Ya kuma kara da cewa, yayin aikin bincike a gidan, jami'an tsaro sun gamu da kalubale, inda wani bom ya tashi amma bai jikkata kowa ba.

Karin bayani