Ana zanga zanga mafi girma a Aleppo dake Syria

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption zanga zangar Aleppo

Zanga zanga ta watsu a fadin Syria inda masu fafutuka yan adawa suka kiran wannan ranar a matsayin wata rana ta bada gudun mawa ga dalibai na Aleppo.

Makwanni biyu da suka wuce an kashe dalibai hudu yayinda dakarun gwamnati suka farma Jamiar Aleppo abunda ya dada jawo zanga zanga a garin kasuwanci na Syria.

Aleepo dai shine babban gari a Syria, cibiyar kasuwanci. Anyi ta zanga zanga a birnin tun shekarar da ta gabata amma ba kamar yadda akeyi a wasu yankunan a Syria ba.

Amma zanga zangar wannan satin ta kai girman gaske. Masu fafutuka na cewa wannan itace mafi girmar zanga zangar da suka gani a Aleppo.

Karin bayani