Harba wani kunbom Amurka ya ci tura

Yunkurin tada kumbo Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Yunkurin tada kumbo

An dakatar da yunkurin farko da aka yi na harba kunbon jigila zuwa sararin samaniya da kamfani mai zaman kansa ya kera.

Ya yi lodin kayayaki da za kai tashar bincike ta kasashe da ke sararin samaniya.

An kashe injin kumbon ne a daidai lokacin da zai daga din daga Cape Canaveral, a jihar Florida ta Amurka.

Kwamfutocin da ke cikin kumbon ne suka lura da matsala a karfin motsin daya daga cikin injinansa.

Kumbon, wanda ba a ba shi suna ba, kirar wani kamfani njihar Carlifornia mai suna Space-X, an yi nufin ya kai ton talatin ne na abinci da sauran kayayyaki zuwa tashar binciken.

Karin bayani