Dole turai ta karkata ga bunkasa tattalin arziki - Obama

Shugabannin kasashen G8 Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Shugabannin kasashen G8

Shugaban Amurka Barack Obama ya ce taron kasashen G8 ya samu nasara a kokarin ceto tattalin arzikin duniya daga durkushewa.

Shugaban, wanda ya bayyana hakan bayan taron shugabannin kasashen takwas na G8 da aka gudanar a wajen shakatawa na Camp David a Amurka, ya ce dukkan shugabannin sun amince cewa, bunkasa tattalin arziki da kuma samar da ayyukan yi su ne abinda za su sa a gaba.

Sai dai shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta dage cewa, dole ne kasashen Turai su ci gaba da shirinsu na tsuke bakin aljihu.

Sanarwar karshe ta bayan taron ta ce matakan bunkasa tattalin arziki ka iya bambanta daga wannan kasar zuwa waccan.

Shugabannin sun kuma amince kasar Girka ta ci gaba da kasancewa cikin kasashen da ke amfani da kudin Euro.

Murna

Shugaba Obama ya ce ya yi murna ganin cewa an samu muhimmin ci gaba a taron da shugabannin kasashen G8 suka yi, sai dai ci gaban ba na daukar kwararan matakai kan kalubalen koma bayan tattalin arziki ba ne, face sauyi a irin matakan da kasashen duniya ke dauka wajen tunkarar lamarin.

A yanzu za a fi ba da fifiko ne ga bunkasa tattalin arziki da samar da karin guraben ayyukan yi, maimakon shirin tsaurara tsuke bakin aljihu da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ke zaburarwa.

Samun sabon shugaban kasa a Faransa wanda shi ma yake da irin wannan ra'ayi, ya nuna cewa a yanzu za a iya samun sauyin akalar inda tsarin tattalin arzikin Turai zai karkata.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaba Obama

Duk da cewa Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, wadda take sha'awar kwallon kafa, kuma kungiyar Bayern Munich ta kasar ta ta sha kaye a hannun Chelsea ta Ingila a daidai lokacin da ake kammala taron na G8, ba ta sha kaye ba a taron, amma da alama ta koma kokarin kare matsayinta, inda ta hakikance cewa dole a ci gaba da daukar matakan tsuke bakin aljihu.

A yanzu hankali ya karkata zuwa birnin Chicago mahaifar shugaban Amurka Barack Obama, inda akasarin shugabannin kasashen G8 za su halarci taron kungiyar NATO.

Kungiyar tana son duba tsarin mika ragamar samar da tsaro a kasar Afghanistan zuwa ga dakarun kasar.

Za kuma su duba irin rawar da ya kamata kungiyar ta NATO ta ci gaba da takawa bayan ta kawo karshen ayyukanta a can a shekarar 2014.

Sakatare Janar na kungiyar ta NATO Anders Fogh Rasmussen ya ce kungiyar ta Nato a yanzu tana son mambobinta su bi a sannu wajen janyewa daga kasar ta Afghanistan

Karin bayani