Sudan na zargin ana taimakawa Sudan ta Kudu

Tsohon shugaban kasar Afirka ta Kudu Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Tsohon shugaban kasar Afirka ta Kudu

Dakarun gwamnatin Sudan sun saki wadansu 'yan kasashen waje guda hudu wadanda aka kama makwanni ukun da suka wuce.

Ana zargin mutanen hudu, 'yan kasashen Burtaniya da Afirka ta Kudu da Sudan ta Kudu da kuma Norway, da yin wadansu abubuwa da ake tababa a kansu a kusa da wani filin daga.

A watan da ya gabata ne dakarun Sudan ta Kudu suka kwace yankin Heglig da ke da rijiyoyin mai, abin da ya haddasa kazamin fada.

Sudan na zargin mutanen da yi mata zagon kasa a madadin Sudan ta Kudu, zargin da wani kakakin sojin Sudan ta Kudun ya musanta.

Yanzu haka dai an mika mutanen hudu ga babban mai shiga tsakanin Sudan da Sudan ta Kudun wato tsohon shugaban kasar Afirka ta Kudu, Thabo Mbeki.

Karin bayani