Anwar Ibrahim na fuskantar aikata miyagun laifufuka

Anwar Ibrahim Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Anwar Ibrahim

Jagoran 'yan adawa a Malaysia, Anwar Ibrahim zai fuskanci tuhumar aikata muggan laifuka saboda irin rawar da ya taka a jerin gwanon nuna adawa da gwamnati.

Ana masa wannan tuhuma ne dai yayin da zaman dar-dar ta fuskar siyasa ke karuwa a kasar gananin zaben dake tafe:

Wakilin BBC ya ce Anwar Ibrahim ya shafe shekaru shida a gidan kaso bisa laifin aikata luwadi, kuma ya jima yana zargin gwamnati da yi masa bi-ta-da-kulli.

Lauyoyi sun ce ana tuhumarsa ne da da keta dokar gwamnati da ta haramta yin gangami bayan ya yi jawabi ga jerin gwanon masu neman a yi zabe na gaskiya a kasar.