An tuhumi Abdallah el Senoussi a Mauritania

Abdallah el Senoussi
Image caption Abdallah el Senoussi

Wani jami'in sharia na Mauritania ya ce, an tuhumi tsohon babban jami'in leken asiri na gwamnatin marigayi Gaddafi, Abdallah El Sanusi da laifin shiga kasar da takardun jabu.

An dai tsare Abdallah El Sanusi yayin da ya shiga kasar da fasgo din bogi a watan Maris.

Tuni dai gwamnatin Libya, da ta Faransa da kuma kotun hukunta manyan laifuka ta duniya, wato ICC suka nemi a mika mu su shi.

Abdallah El Sanusi dai na hannun daman Kanar Gaddafi ne, kuma 'yan Libya da dama sun tsane shi, saboda suna dauka cewa shi ne ya aikata yawancin laifufukan keta hakkin bil'adama a lokacin mulkin na marigayi Gaddafi.

Karin bayani