Tashin hankalin Syria ya yadu zuwa Lebanon

Daya daga cikin ababen hawan da aka kona Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Daya daga cikin ababen hawan da aka kona

Tashin hankalin kasar Syria ya yadu zuwa Lebanon inda aka yi fito-na-fito cikin dare tsakanin magoya bayan Shugaba Bashar al-Assad da masu adawa da shi.

Mutane da dama ne dai aka ba da rahoton cewa sun rasa rayukasnu a unguwannin da 'yan Sunni suka fi yawa.

Rikicin ya barke ne sakamakon harbe wasu manyan malaman Sunna biyu wadanda ke da alaka da masu adawa da Syria da sojojin Lebanon suka yi ranar Lahadi.

A karon farko rikicin ya yadu zuwa Lebanon tun lokacin da aka fara shi a Syria a watan Maris din shekarar da ta gabata.

Kisan da aka yi wa malaman biyu, wadanda aka alakanta da masu fafutuka da ke adawa da gwamnatin Syria a karkashin jagorancin Saad al-Hariri, ya janyo mayar da martani cikin fushi a yankunan da mabiya Sunna suka fi yawa.

A wurare da dama, an datse manyan hanyoyi ta hanyar kona tayoyin mota, daga bisani jami'an tsaro sun shiga tsakani inda suka bude hanyoyin.

Sai dai an gwabza mummunan fada a kudancin birnin Beirut tsakanin mabiya Sunna da ke da mabanbantan ra'ayi kan gwamnatin Syria.

Wasu 'yan bindiga da ke biyayya ga Saad Al hariri sun kai hari a kan ofisoshin wani jagora da ke goyon bayan gwamnatin Syria.

Sai dai rikicin ya lafa bayan da jagoran, Shaker Berjawi, ya bar yankin, kuma sojojin Lebanon suka shiga.

Mallaman na Sunna da kuma shugabannin siyasa sun yi kiran da a kwantar da hankula, kuma tuni aka kaddamar da bincike don gano musabbabin kisan malaman Sunnar su biyu a wajen binciken motoci na sojin Lebanon.

Martanin da lamarin ya janyo ya kara bayyana wa a fili irin rarraburwar da ake da ita a Lebanon kan rikicin Syria da kuma yadda hakan ka iya rikidewa zuwa tashin hankali cikin kankanin lokaci.

Karin bayani