ECOWAS ta cimma yarjejeniya da sojojin Mali

Wani Sojan Mali a filin saukar jiragen sama Hakkin mallakar hoto x
Image caption Wani Sojan Mali a filin saukar jiragen sama

A kasar Mali, an cimma matsaya tsakanin masu shiga tsakani na kungiyar ECOWAS da jagororin sojojin da suka yi juyin mulki a kan tsawaita wa'adin gwamnatin rikon kwaryar kasar karkashin jagorancin Shugaba Dioncunda Traore.

Sojojin da suka yi juyin mulki sun yi ta nuna adawa da tsawita wa'adin, sai dai bayan barazanar kara kakaba musu takunkumi, sojojin sun bayar da kai bori ya hau.

Daya daga cikin masu shiga tsakani na kungiyar ECOWAS, wanda har wa yau shi ne ministan harkokin wajen Burkina Faso, Djibrill Bassole, ya ce a karkashin yarjejeniyar, jagoran sojojin da suka yi juyin mulki a watan Maris din da ya gabata, Captain Ahmadu Sanogo, zai samu matsayin tsohon shugaban kasa.

Kuma za a bashi dukkan wata alfarma da ke tattare da hakan.

Shugabannin kasar ta Mali da masu shiga tsakani na ECOWAS, sun kuma amince da wa'adin mika mulki ga zababbiyar gwamnatin demokradiya a kasar nan da shekara guda.

A baya dai jagororin juyin mulkin sun kafe a kan cewa tunda kundin tsarin mulkin kasar ya ce dole ne a gudanar da sabon zabe a cikin kwanaki arba'in, gwamnatin rikon kwaryar ba za ta zarta kwanaki arba'in ba, yayinda sauran bangarorin suka ce ba yadda za a iya zabe cikin kwanaki arba'in.

Hakan ta sa wakilan ECOWAS suka ce abin da ya fi kusa da tanade-tanden tsarin mulkin kasar shi ne jagoran majalisr dokokin kasar ya rike mulki har a gudanar da sabon zabe, daga karshe an amince da hakan.

Abinda har yanzu bai fito fili karara ba shi ne, irin rawar da sojoji za su taka a gwamnatin rikon kwaryar, da kuma yadda bangarorin za su tunkari batun arewacin Mali inda 'yan tawayen Abzinawa suka ayyana 'yancin kansu.

Karin bayani