An kashe sojoji da dama a Yemen

Sojojin Yemen
Image caption Sojojin Yemen

An hallaka sojoji akalla casa'in a wani harin kunar bakin wake da aka kai a Sana'a, babban birnin Yemen, yayin shirye-shiryen wani atisayen soja.

Wasu mutanen da dama sun jikkata yayin da bam din ya fashe a kusa da fadar shugaban kasar.

Rahotanni dai na cewa, dan kunar bakin waken yana sanye ne da kakin soja.

Wannan shine hari mafi girma da aka kai a Sanaa, tun lokacin da Shugaba Abd-Rabbuh Mansour Hadi ya hau mulki a cikin watan Fabrairu.

Kungiyar Alqa'ida dai tace itace ta kai harin.

Wakilin BBC yace, wannan harin wani kwakwkwaran sako ne zuwa ga sabon shugaban kasar, kuma yana nuna cewa, akwai jan aiki sosai a kokarin kawar da Al Qaeda daga Yemen.

Karin bayani