Cin zarafin mata ta zama wata gagarumar matsala a duniya

Wani namiji na dukar matarsa
Image caption Wani namiji na dukar matarsa

A Amurka wata kungiya ta yi kiran da a sanya irin cin zarafin dake faruwa tsakanin iyalai a matsayin wata gagarumar matsala ta shafi duniya baki daya.

Kungiyar ta International Rescue Committee ta ce, ana yin buris da matsalar ta cin zarafi a cikin gida, inda ake daukar matsalar tamkar wani abu da bai kamata a sa baki a ciki ba.

Rahoton ya kuma ce, lamarin ya fi kamari ne ga mata a kasashen Liberia, da Ivory Coast da kuma Saliyo.