Matsalar kasashen Euro na yin barazana ga duniya

Tambarin kudin Euro
Image caption Tambarin kudin Euro

Kungiyar hadin kai ta fuskar tattalin arziki wato OECD ta yi kashedin cewa, matsalar bashi da ta dabaibaye kasashen dake amfani da kudin Euro ta zama wata babbar barazana ga kokarin farfado da tattalin arzkin kasashen duniya.

Kungiyar ta OEDC ta kuma ce duk da cewa an toshe kafofi da dama dake barazana ga tattalin arzikin duniya, har yanzu akwai yiwuwar gwamnatoci su kara cin bashi, bankuna kuma zasu kara rauni:

Wakilin BBC ya ce, kungiyar ta OECD ta kuma ce ya kamata babban bankin kasashen Turai ya dawo da saye bashin dake bin gwamnatoci.

Karin bayani