EFCC ta karbi rahoton badakalar kudin tallafin man fetur

Shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya

Shugaba Goodluk Jonathan na Nigeria ya mikawa hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasar wani rahoto na bincike kan tallafin man fetur da ake cece kuce a akai.

Rahotanni na cewa shugaban ya mikawa hukumar rahoton zargin sama da fadi na dalar Amurka kimanin Biliyan takwas don ta bincika tare da daukar matakin shari'a a kan duk wanda aka samu da hannun a cikin badakalar.

A cikin watan da ya wuce ne dai wani kwamitin majalisar wakilai ta Najeriya a kan kudaden tallafin man fetur ya gano cewar almubazzaranci da kuma satar da dillalan mai da kuma jami'an gwamnati suka yi ya sa gwamnati ta rasa Dala biliyan kusan 7, wato kwatankwacin kashi daya cikin hudu na kasafin kudin shekara na kasar.

Karin bayani