'Fiye da rabin magungunan Malaria jabu ne'

Hakkin mallakar hoto Science Photo Library
Image caption Sauro ne kawo cutar malaria

Wani sabon bincike ya gano cewa gagarumar nasarar da aka samu ta baya-bayan nan a yakin da ake yi da zazzabin cizon sauro, wato malaria, na fuskantar barazana, saboda kusan sulusin magungunan cutar da ake sayarwa a yankunan Kudu maso Gabashin Asiya da Afirka Kudu da Sahara ko dai na jabu ne ko kuma ba su kunshi kayan hadi da ba na gari ba.

Masu bincike sun ce yayin da magunguna na jabu ke barazana ta da-gamo-da-kasawa ga lafiya, magungunan da ba su da inganci kuma suna karawa cutar karfin jurewa magani.

A cewarsu wajibi ne hukumomin da alhakin abin ya rataya a wuyansu su kara kaimi don ganin an kawar da magunguna na jabu an kuma tabbatar da bin kai'da yayin harhada magunguna.

Masu binciken wadanda suka duba samfuri dubu daya da dari biyar na magungunan malaria dabam-daban har bakwai daga kasashe bakwai na kudu maso gabashin yankin Asia, sun ce magunguna marasa inganci da ma na jabu, na janyo kwayoyin cutar ta Malariya suna bijirewa magunguna da ma rashin warkewa daga cutar ga wadanda suka harbu.

Bayanai daga kasashe ashirin da daya a Afrika kudu da hamada da suka kunshi samfurin magunguna dubu biyu da dari biyar sun nuna sakamako makamancin hakan.

Kwararru sun ce, binciken cututtuka masu yaduwa da aka wallafa a mujallar kiwon lafiya ta The Lancet, wani hannunka mai sanda ne.

Masu binciken daga cibiyar Fogarty ta Amurka, sun ce akwai yiwuwar girman matsalar ya fi iya abin da suka gano.

Ba a dai gudanar da wani bincike mai girma a kasashen China ko India ba, kasashen da ke dauke da kashi daya bisa uku na al'ummar duniya, kuma ka iya zama tushen magungunan jabu masu yawa da ma magunguna masu inganci.

Karin bayani