NATO za ta mika ragama ga dakarun Afghanistan

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wani hari da kungiyar tsaro ta NATO ta kai

Shugaba Obama na Amurka ya ce bakin kungiyar tsaro ta NATO ya zo daya a kan shirinta na danka jagorancin yakin Afghanistan a hannun 'yan kasar ta Afghanistan nan da tsakiyar shekara mai zuwa.

Da yake rufe taron kolin kungiyar da abokan huldarta a Chicago, Mista Obama ya ce a tsakiyar badin ne dakarun NATO za su mai da hankali ga aikin ba da horo da kuma tallafi yayinda suke kammala shirye-shiryen janyewa a karshen 2014.

Ya ce tun a bara muka fara mayar da wasu sassan Afghanistan hannun dakarun tsaro na kasar, al'amarin da ya baiwa dakarunmu damar fara dawowa gida.

Shugaban na Amurka ya baiwa kasar ta Afghanistan tabbacin cewa dangatakarta da NATO ta fuskar tsaro za ta ci gaba har bayan janyewar.

Sai dai ya bayyana karara cewa, ba a kai ga cimma yarjejeniya da Pakistan ba kan batun sake bude hanyoyin isar da kayayyaki ga dakarun NATO a Afghanistan

"Ba mu yi tsammanin za a warware batun bude hanyar isar da kayayyakin ba a wannan taron na Chicago ba. Sai dai muna samun ci gaba kan batun," in ji shugaba Obama

Karin bayani