Ana zaben shugaban kasa a Masar

Zaben shugaban Masar Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Zaben shugaban Masar

Miliyoyin masu kada kuri'a ne suka fara tudada zuwa rumfunan zabe ranar Laraba a kasar Masar, domin zaben sabon shugaban kasar, wanda ake ganin shi zai kasance sahihin zaben shugaban kasar a karon farko cikin tarihi.

'Yan takara goma sha biyu ne ke fafatawa a zaben da za a shafe kwanaki biyu ana yi kuma ana sa ran masu kada kuri'a miliyan 50 ne za su yi zabe.

Idan ba a samu dan takara daya da ya yi zarra ba, to 'yan takara biyu da suka fi samu kuri'a za su je zagaye na biyu.

Ta yiwu ba za a samu sakamako na karshe ba har sai cikin wata mai zuwa.

Yau dai rana ce mai dimbin tarihi ga 'yan kasar Masar.

A karon farko cikin tarihin kasar da ya zarta shekaru dubu biyar, sun samu damar zaben shugaban kasar su ba tare da tursasa wa ba.

Za a bude rumfunan zabe har tsawon kwanaki biyu.

Idan babu dan takarar da ya samu fiye da rabin kuri'un da aka kada, za a je zageye na biyu a wata mai kamawa.

Mutane hudun da ake ganin su ne na gaba-gaba a zaben, ko dai masu kishin addinin Musulunci ne ko kuma tofaffin ministoci da suka rike mukami a gwamnatin da ta shude.

Masu ra'ayin raba siyasa da addini da suka jagoranci zanga-zangar da ta kai ga tumbuke shugaba Hosni Mubarak, basu samu sukunin fitar da dan takarar da yake da karsashi ko kuma yake da tsarin da zai ja hankalin 'yan kasar Masar ba.

Kasar ta Masar da sabon shugabanta da za a zaba, za su fuskanci kalubale mai girma.

Image caption Zaben shugaban kasa a Masar

Dole ne shugaban ya fito da hanyoyin sake samar da tsaro ga al'ummar Masar.

Kasar tana bukatar garambawul a hukumar 'yan sandanta domin magance karuwar aikata laifukan da ya biyo bayan rushewar rundunar 'yan sandan kasar karkashin gwamnatin da ta gabata, wacce ake zargi da cin hanci da kuma musguna wa al'umma.

Tattalin arzikin kasar a yanzu ba zai iya biyan bukatar matasa da ke kara yawa a kasar ba.

Sannan akwai yiwuwar a samu tankiya da rundunar sojin kasar, wadda da alama ke son ci gaba da rike matsayinta na mai fada a ji a kan shugabancin kasar.

Masu zabe dai ba su san wanne irin iko sabon shugaban zai samu ba, domin har yanzu suna jiran a bayana su cikin sabon kundin tsarin mulkin kasar.

Sai dai a kan titunan birnin alkahira, wata bukata ta bai daya ita ce, a kawo karshen tarzoma da rudani da kuma rashin tabbas da kasar Masar ke fama da su tun da aka hambarar da gwamnatin shugaba Mubarak a watan Fabrairun da ya gabata.

Karin bayani