Takaddamar launin fata kan gasar Eurovision a Ukraine

eurovision Hakkin mallakar hoto gattana
Image caption Mahaifin Gaitana dan kasar Congo ne yayin da mahaifiyarta ta fito daga Ukraine

Wani abu da aka tsara domin shakatawa, gasar wake-wake ta Turai ta saba haifar da cece-kuce a kusan dukkan lokuta.

Haka kuma lamarin yake a wannan karon a kasar Ukraine, inda batun wariyar launin fata ya mamaye shirye-shiryen gasar.

Jam'iyyar 'yan mazan jiya ta Freedom Party, ta yi Allah wadai da zaben Gaitana - wacce ke da tsatson kasar Congo - domin ta wakilci Ukraine.

"Miliyoyin mutanen da za su kalla, za su ga cewa wata da bata da alaka da jinsinmu ita ce ta wakilce mu,"a cewar Yuri Syrotyuk, wanda jam'iyyarsa ke shirin shiga zaben 'yan majalisar dokoki a bana.

"Za a fara kallon Ukraine a matsayin wata da ta samo asali daga wani loko a nahiyar Afrika".

An soki kalaman

Daga bisani ya ki amince wa da kalaman wariyar launin fata, inda yace yana sukar "rashin adalci ne wurin zaben".

Sai dai kusan dukkan jam'iyyun siyasa da kuma shahararrun mutane harda 'yan damban ne Vitaly da Volodymyr Klitschko, sun yi watsi da kalaman nasa.

Gaitana, wacce za ta shiga zagayen kusa da na karshe ranar Alhamis, ta ce lamarin ya nuna yadda batun wariyar launin fata ke karuwa a Ukraine.

"Na ji kunya sosai kan wannan abinda ya faru, saboda Ukraine kasa ce mai bin tafarkin demokuradiyya, inda mutanen da suka san mutuncin juna suke zaune," a cewarta.

'Hada al'adu biyu'

Mahaifin Gaitana wanda dan kasar Congo ne, ya yi karatu a Kiev, babban birnin kasar Ukraine, inda ya hadu da mahaifiyarta.

Jim kadan bayan haihuwarta a 1979, sai suka koma Congo-Brazzaville, inda suka zauna tsawon shekaru biyar.

Sai dai daga bisani aurensu ya mutu, kuma mahaifiyar Gaitana ta koma da ita Ukraine.

Lokacin da take yarinya mahaifinta ya sanya mata sha'awar wakokin Diana Ross, Stevie Wonder, Michael Jackson, Lionel Richie da makamantansu.

Tana kallon kanta a matsayin wacce ke dauke da tsatson al'adu biyu - sannan ta ce kawayenta a Congo suna jin dadin wakokinta da cewa na Afrika ne.