Ana tattaunawa a Bagadaza kan shirin nukiliyar Iran

Shugaba Ahmadinejad yana ziyarar wata masana'antar nulkiya Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugaba Ahmadinejad yana ziyarar wata masana'antar nulkiya

Manyan kasashen duniya shidda sun gabatarwa Iran wani sabon tayi a kokarin rage fargaba dangane da shirinta na nukiliya.

Kakakin kungiyar kasashen Turai a wurin taron da ake yi a birnin Baghadaza na Iraqi, ya ce bai fayyace ko tayin da za'a yiwa Iran zai hada da sassauta takunkumin da aka kakaba ma ta ba.

Tuni dai ministan hulda da kasashen waje na Rasha, Sergei Lavrov ya ce, an soma wannan tattaunawa da kafar dama.

Mr Lavrov ya kara da cewa ya kamata a gane cewa warware wannan batu ba zai zama tamkar sha yanzu, magani yanzu ba, dole sai an bi matakai, kuma idan aka yi abin cikin tsanaki da mutunci to za'a cimma nasara.

Karin bayani