An kashe mutane biyu a Sakkwaton Najeriya

Wasu jami'an tsaro a Najeriya Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wasu jami'an tsaro a Najeriya

'Yan Sanda a birnin Sakkwaton Najeriya sun tabbatar da mutuwar mutane biyu a wani hari da wasu 'yan bindiga suka kai a kusa da ofishin mataimakin babban sufetan 'yan sandan kasar da sanyin safiyar yau.

Wadanda suka shaida lamarin sun ce maharan sun je ne a cikin wata karamar mota da kuma babur.

Birnin na Sakkwato na daga cikin wadanda suka fi kwanciyar hankali a kasar a baya, amma kuma ya fara fuskantar kalubalen tsaro tun bayan kisan wasu turawa biyu da aka yi garkuwa da su.

Rundinar 'yan sandan jihar ta Sakkwato dai ta ce tana gudanar da bincike a kan wannan lamari.

Karin bayani