Jami'an Kenya zasu fuskanci kotun ICC

kenyata Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Mataimakin Pirayi Ministan Kenya, Uhuru Kenyata

Kotun hukunta miyagun laifufuka ta duniya, ICC ta yi watsi da karar da wasu fitattun 'yan Kenya hudu suka daukaka, bayan da aka zarge su da aikata laifufukan cin zarafin Bil-Adama.

Mutanen hudu da suka hada da mataimakin Pirayi ministan kasar, Uhuru Kenyatta da tsohon minista William Ruto, sun kalubalanci hurumin kotun ne na yi musu sharia bisa zargin kitsa tashin hankalin da ya biyo bayan zaben shugaban kasa da na 'yan majalisar dokoki da aka yi a Kenyar a shekara ta 2008.

Hakan dai yana nufin yanzu kotun ta ICC za ta tsaida ranar da mutanen hudu za su gurfana a gaban ta a birnin Hague.

Ana dai sa ran duka Mr Uhuru da Mr Ruto za su tsaya takara a zaben shugaban kasar na badi.

Karin bayani