Matsalar abinci a Nijer ta hana yara karatu

nijer Hakkin mallakar hoto Oxfam
Image caption Yara masu fama da yunwa a Nijer

Wani rahoto da kungiyar agaji ta World Vision ta wallafa, ya ce matsalar karancin abincin da ake fama da ita a wasu sassan Jumhuriyar Nijar, ta sa yara 'yan makaranta da dama suna barin karatunsu.

Matsalar ta tilastawa wasu kananan aikace-aikace a cikin garuruwa da birane da nufin samun abun da zasu taimaka a iyayensu.

Rahoton ya ce a yankin Tillabery kadai dake arewa maso yammacin Nijar din, yara dubu goma sha shida ne suka samu kansu a cikin irin wannan hali.

Rahoton ya kara da cewar wasu iyaye suna aurar da 'ya'yansu maata da basu wuce shekaru bakwai zuwa takwas ba, saboda kawai basu da halin da zasu ciyar da su.

Karin bayani