Pillay ta bukaci a janyewa Zimbabwe takunkumi

mugabe Hakkin mallakar hoto ap
Image caption Shugaban Zimbabwe, Robert Mugabe

Shugabar hukumar kare hakkin bil adama ta Majalisar Dinkin Duniya, Navi Pillay, ta yi kira ga dukkanin bangarorin da basa ga maciji da juna a gwamnatin hadakan zimbabwe dasu amince da muhimman sauya sauye in dai har ana so a kaucewa wani tashin hankalin zabe.

Navi Pillay na wata ziyara ce a Zimbabwe inda ta kuma yi kira ga kasashen yammacin duniya da su janye takunkumin da suka sanyawa shugaba Mugabe da sauran mukarraban sa.

Navi Pillay ta kuma yi gargadin cewa, idan dai ba a samu canji da sauri ba, to zabe mai zuwa, wanda kila za ayi a cikin wannan shekarar, zai fuskanci irin tashin hankalin da aka gani a zaben shekara ta 2008.

A zabukan da aka gudanar a baya, an zargi magoya bayan Shugaba Mugabe da kashe mutane harma da duka da kuma gallazama daruruwan mutane.

Tun daga lokacin ne dai aka tilastawa Mr Mugabe ya raba mukamin gwanmnati da masu hamayya dashi, abinda yasa Morgan Tsvangirai ya zama Pirayi Minista.

Navi Pillay ta kuma roki kasashen yammacin duniya da su dakatar da sakawa kamfanoni da mutanen dake mu'amulla da Zimbabwen takunkumin tattalin arziki, tana mai nuni da cewa abin na komawa kan talakawa ne -- zargin da tuni Burtaniya da wasu kasashe suka musunta.

Karin bayani