Amurka za ta janye tallafi zuwa Pakistan

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Sakatariyar harkokin wajen Amurka, Hillary Clinton

Sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton ta soki daure wani likita dan Pakistan da ya taimaka wa Hukumar tsaro ta CIA wajen gano inda Osama Bin Laden ya ke a Pakistan.

An daure Dr Shakil Afridi a ranar Laraba na tsawon shekaru 33 saboda ya hada wani shirin rigakafin bogi domin gano kwayoyin hallittun iyalan Osama Bin Ladan.

Kwamitin kasagin kudin Amurka na Majalisar Dattijai ya yanke duk wata gudunmuwa ko agaji da kasar ke baiwa Pakistan saboda hukuncin da ta dauka.

Hillary ta ce Amurka ta nuna damuwa ga daurin da aka yi wa Dr Afridi da kuma hukuncin mai tsananin da aka yanke a kan likitan.

Ta ce Amurka za ta ci gaba da kalubalantar hukuncin da hukumomin Pakistan su ka dauka a kan sa.

A Majalisar Dattawan Amurka haka zancen ma ya ke, domin sun nuna matukkar damuwa ga matakin da Pakitsan din ta dauka, abun da har ma ya sanya kwamitin kasafin kudin Majalisar ya rage tallafin da kasar za ta bai wa Pakistan da dala miliyan talatin da uku cikin dala biliyan guda da kasar ta yi alkawarin za ta bai wa Pakistan a badi.

Kwamitin ya ce kowani miliyan guda na matsayin kowacce shekara da aka yankewa Dr Afridi.