Ana gwabza kazamin fada a Congo

Dakarun gwamnatin DRC
Image caption Dakarun gwamnatin DRC

Rohotanni daga Jamhuriyyar Demokradiyyar Kongo na cewa ana can ana karawa a gabashin kasar tsakanin dakarun gwamnati da wani gungun dakarun da suka sauya sheka.

Fandarraun sojojin sun ce su 'yan wata kungiyace da ake kira March 23r Movement wadda ta samo asali daga wata kungiyar Tusti ta CNDP mai dauke da makamai.

Tun kwanaki goma da suka wuce ne dai aka fara fada a yankin Nord Kivu da manayn makamai. MDD tace dubban mutane dai suka tserewa fadan, inda suka shiga Uganda da Rwanda

Karin bayani