Ba zamu yarda a raba kasar nan ba- Gowon

Hakkin mallakar hoto leadership
Image caption Tsoho Shugaban, Najeriya, Janar Yakubu Gowon

Tsohon shugaban Najeriya Janar Yakubu Gowon ya nemi kungiyar jama'atu Ahlul sunna lilda'awati wal jihad wadda aka fi sani da Boko Haram ta koma kan teburin sulhu da gwamnatin kasar.

Tsohon shugaban ya ce kamata ya yi kungiyar ta bayyana bukatunta da nufin kawo zaman lafiya a kasar.

Ya ce; " Ban yarda da abun da wasu ke cewa wai talauci ne ke haddasa Boko Haram.

"A duniya gabaki daya, babu inda talaka ke daukar makami ya hallaka dan uwansa.

"Na san gwamnati ta na iya kokarinta wajen ganin an samar da tsaro, amma ya kamata shugabanin kungiyar su fito su bayyana bukatunsu."

Tsohon Shugaban kasar ya ce yana goyon bayan sulhu, amma ba zai taba amicewa da abun da zai kawo rabuwar Najeriya ba.

"Babu shugaba ko gwamnati da za ta taba amincewa da rabuwar Najeriya." In ji Gowon