'Yan tawayen Mali sun hada kai domin kafa kasar Islama

Hakkin mallakar hoto AFP

Kungiyoyin 'yan tawaye a Mali sun amince su hade wuri guda domin kafa kasar Islama mai cin gashin kanta a arewacin kasar.

An dai ji karar harbe-harben murnar bayan da 'yan tawayen su ka amince da yarjejeniyar a biranen da su ke da iko, wanda su ka hada Timbuktu.

'Yan tawayen sun bayyana hadewarsu ne bayan wata tattaunawa da aka yi tsakanin kungiyar Islama ta Ansar Dine da kuma kungiyar ci gaban abzunawa ta Azawad.

Wani mai magana da yawun Ansar Dine cewa ya yi bangarorin sun amince su yi aiki tare domin kafa yankin Islama mai zaman kansa a arewacin kasar Mali.

A baya dai an samu rashin jituwa tsakanin bangarorin biyu a yayinda kowace kungiya ke kokarin kwato na ta garin.

A yanzu haka dai sun amince ne su hade wuri guda garuruwan da si ka kwato a arewacin kasar bayan juyin mulkin da aka yi a babban birnin kasar Bamako.