An hallaka sama da mutane 90 a Syria

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

Masu fafutukar kare yancin dan adam a Syria na ba da rahotannin cewa, jami'an tsaro sun yi kisan gilla a garin Houleh da ke yankin Homs.

Wata babbar kungiyar masu fafutukar ta ce an kashe sama da mutane 90 wadanda yawancin su yara ne da mata a lokacin da dakarun gwamnatin ke kaiwa yankin hari a yayinda kuma da dama daga cikin mazaunin garin su ka tsere.

Wasu hotunan bidiyo da ba'a tantance ba da aka sanya a shafin Internet sun nuna gawawwakin yara jina-jina a kasa a yayinda wasu mutane ke rusa ihu.

Masu fafutukar kare hakkin dan adam sun ce Iyalai da dama ne jami'an tsaro su ka hallaka a bayan gari.

Wasu kuma sun mutune saboda ruwan bama-baman sa ake jefawa garin.

Idan dai har an tantance adadin mutanen da masu fafutuka su ka ce an kashe a garin, to ranar ce mafi muni a tashin hankalin da ake yi a kasar, tun bayan da aka tsagaita wuta kusan makonni shida da su ka wuce kenan.

A yanzu haka dai ana kallon tsagaitun wutan da aka yi a kasar a matsayin tatsuniya ganin cewa akwai jami'an Majalisar Dinkin Duniya masu sa'ido a kasar kusan dari biyu da sittin a kasar amma dai an samu raguwar tashin hankalin a yawancin inda wadannan mutane suke.