An kashe kananan yara da dama a Syria

Masu zanga zanga a Syria Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Masu zanga zanga a Syria

Shugaban tawagar masu sa ido na Majalisar Dinkin Duniya a Syria, ya yi allawadai da abinda ya kira rashin imani na kashe kashen da akai jiya juma'a a garin Houla dake kusa da birnin Homs.

Yanzu haka masu sa ido na MDDn sun je wajen da lamarin ya faru, wanda masu fafutuka suka kira da kisan kiyashin da dakarun gwamnatin Syrian suka yi.

Tuni kuma masu zanga zanga suka fara kira ga kasashen waje da su dau matakin kare fararan hular Syria.

Hotunan bidiyon da masu mafutuka suka sa a internet ko yanar gizo sun nuna karara irin akubar da aka ganawa jama'a a garin Houla, inda aka nuna kananan yara da dama da aka kashe.

Ana jin muryar wani mutum na ihu cewa duka kananan yara ne da dama kuma ana daga kawo wasu.

Masu sa ido na MDDn da suka ziyarci garin daga baya sun tabbatar da labarin da masu fafutukar suka bayar. Manjo janar Robert Mood shi ne shugaban masu sa idan: Clip:" Ya ce yau da safe tawagar ta je wajen kuma sun kawo mun rahotan cewa sun kirga kuma za mu iya tabbatar da cewa kananan yara 32 'yan kasa da shekaru 10 sannan da wasu karin manya 60 aka kirga matattu".

Sai dai kuma dayawan 'yan garin sunji haushi kan cewa masu sa idan ba su yi wani abu ba dan hana afkuwar abin da suke kira kisan kiyashi.

Inda suka ce tun alokacin da abin ke faruwa suka sanar da su, amma ba wanda amma ba wanda ya kai musu dauki.

Masu fafutuka sun ce ruwan albarusan da akai ne aka kashe wasu daga cikin mutanan, wasu kuma kisan gilla ne mayakan sakai na gwamnatin da ake kira Shabbiha sukai musu.

An yi ta zanga zanga a wasu sassan kasar ta Syria bisa abin da ya faru a Houla, wasu kuma sukai a wajen jana'izar mutanan da aka kashe bayan sallar juma'a, ya yin da akai ta karin harbe harbe.

Kungiyoyin 'yan adawa na neman kwamitin sulhu na MDD ya dau mataki kan Syria yayin da ake nuna bakin cikin abin da ke faruwa a kasar a wasu kasashen duniya.

Sai dai kuma har yanzu Rasha na goyan bayan abin da gwamnatin Syrian ke cewa 'yan adawa ne ke takalar dakarun gwamnatin. Har yanzu dai ba batun za'a dau irin matakin da aka dauka a a Libya kan Syrian.

Sai dai kuma za'a iya samun matsain lamba na kara karfafa dakarun 'yan tawayen Syrian.

Karin bayani