'Yan tawayen Mali sun hade

'Yan tawayen Mali Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan tawayen Mali

Kungiyar 'yan tawayen Abzinawa ta MNLA a kasar Mali tare da kungiyar masu kishin Islama ta Ansarudeen sun amince su hade domin kafa kasar musulunci mai cin gashin kanta a arewacin kasar, yankin da suka kwace a farkon wannan shekarar.

Duka bangarorin biyu sun yi sassauci akan matsayar su, inda kungiyar Ansaruddeen ta amince ta yi kokawar kwatar 'yancin kai, su kuma 'yan tawayen Abzinawan suka yadda a kafa kasar musulunci.

Wani kakaakin Azibinawan dake tawaye a Mali, Moussa Ag Assarid ya yiwa BBC karin bayani akan yarjejeniyar da suka kulla da wata kungiya mai kaifin kishin Islama a kasar ta Ansarruddin ta hadewa don su kafa daular musulunci a arewacin kasar.

Moussa Ag Assarid yace gaskiya ne cewa a baya muradunsu sun banbanta.

Amma a yau dole ne mu maida hankali akan kawo zaman lafiya a kasar Azawad mai cin gashin kanta, kuma jama'ar kasar sune zasu yanke hukunci akan makomarta.

Karin bayani