Ana nuna goyan baya ga likitocin da aka kora a Lagos

Lagos
Image caption Lagos

Kungiyar maikatan man fetur dana iskar Gas a najeriya wato NUPENG tayi barazanar tafiya yajin aiki saboda likitoci 788 da gwanatin Jahar Lagos tace ta kora daga aiki.

Kungiyar tace ta baiwa gwamnatin Jahar Lagos din zuwa ranar litinin data dawo da su bakin aiki ba tare da wani sharadi ba, idan ba haka ba kungiyar tace zata dakatar da aiki a fadin jahar lagos da kuma kewayenta.

Tun a makwannin baya ne dai likitocin jahar Lagas din suka shiga yajin aiki na har sai yadda hali ya yi, bisa rashin biyansu sabon albashin da suka ce gwamnatin jahar ta yi kamar yadda gwamnatin tarayyar ta amince da shi.

Lamarin da yasa gwamnatin jahar Lagas din daukar wasu likitocin da suka maye gurabensu, ganin irin halin da jama'a suke shiga .

Wannan ne ya sa likitocin shigar da gwamnatin Lagas din kara suna neman da a hanata daukar likitocin da zasu maye gurabansu.

Yanzu haka kuma wasu kungiyoyin a sauran sassan Najeriya su kai barazanar marawa likitocin Lagas din baya ta hanyar tafiya yajin aiki muddin gwamnatin bata mai dasu bakin aikinsubake ta kira ga gwamnatin

Karin bayani