Majalisar Dinkin Duniya na taron gaggawa kan Syria

Gawarwakin mutanan da aka kase a Houla Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Gawarwakin mutanan da aka kase a Houla

Kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya naa wani taron gaggawa akan kashe fararen hular da aka yi a garin Houla na Syria.

Sai Gwamnatin Syria tace bata da hannu a lamarin wanda aka rawaito cewa ya yi ajalin mutane fiye da casa'in a garin, cikin su harda yara kanana.

Wani kakakin ma'aikatar harkokin wajen Syria ya ce yakamata a sani kararara cewa sojojin gwamnati basu da hannu a lamarin. Kuma gwamnati ta yi Allah wadai dashi a matsayin wani aikin tadandanci

Taron ya zo ne bayan Sakataren harkokin wajen Burtaniya, William Hague ya yi kira ga kasashen duniya da su kara matsawa gwamnatin Bashar Al-Assad lamba.

Mista Hague na magana ne gabanin wata ziyara da zai kai Moscow don tattauna kan batun na Syria da mahukuntan Rasha.

Karin bayani