An zargi Rwanda da rura wutar rikicin Congo

Image caption Sojin Rwanda

Majalisar Dinkin Duniya ta ce tana da shaidar cewa tayar da kayar baya a Gabashin Jamhuriyyar Dimokradiyyar Congo na ruruwa ne bisa tallafi da agajin mayaka daga Makwabciyar kasar Rwanda.

BBC ta ga rahoton Majalisar Dinkin Duniyar wanda aka samar bisa tattaunawa da wasu wadanda suka sauya sheka a birnin Goma wanda ya zargi kasar Rwanda da hadin baki na samarda makamai da kuma sojoji ga 'yan tawaye a Jamhuriyyar Dimokradiyyar Congo.

Daya daga cikin sojojin da aka kai iyakar rahoton ya ce yaro ne mai karancin shekaru.

Fada ya barke ne a watan Aprilu bayan da wasu sojoji daga dakarun Congo suka balle a Gabacin kasar.

Wasu daga cikin shugabannin masu boren yan kabilar Tutsi ne wanda ake danganta su da kasar Rwanda, kafin a sa su a rundunar sojin Congo a sheakara ta dubu biyu da tara.

Karin bayani