An fitar da sakamakon shugaban kasar Masar

Mutanan da su kai nasara a zaben shugaban kasar Masar Hakkin mallakar hoto .
Image caption Mutanan da su kai nasara a zaben shugaban kasar Masar

Hukumar zaben kasar Masar ta fitar da sakamakon zaben shugaban kasar wanda shine irinsa na farko mafi inganci da aka taba gudanarwa a kasar.

Hukumar ta tabbatar da cewa Ahmed Shafiq, wanda tsohon Praminista ne a zamanin mulkin Hosni Mubarak, da kuma Mohamed Mursi,dan takarar kungiyar 'yan uwa Musulmi sune 'yan takara biyu da zasu fafata a zagaye na biyu na zaben da za'a gudanar a wata mai zuwa.

Dukkan 'yan takaran biyu dai sun samu fiye da kuri'u miliyan biyar, cikin kuri'u fiye da kashi arba'in cikin dari da suka kada kuri'a.

Hukumar zaben kasar Masar din dai ta yi watsi da korafe-korafen wasu daga cikin 'yan takarar da ke cewa an tabka magudi a zaben.

Karin bayani