Nepal za ta gudanar da zabe

Image caption Nepalese

Prime Ministan kasar Nepal Baburam Bhattarai ya sanar da cewa kasar za ta gudanar da zabuka cikin watanni shida masu zuwa.

Wannan yunkurin ya biyo bayan fadawar da kasar ta Nepal ta yi cikin rikicin siyasa saboda gazawar da aka yi ta cimma matsaya a kan sabon tsarin mulkin kasar.

Wakilai na wata majalisa ta musamman sun yi fafutukar ganin an tsaida shekaru hudu a kokarin sasantawa.

Wa'adin karshe dai ya kare ne a daren jiya Lahadi ba tare da cimma yarjejeniya ba.

Kawunan jam'iyyun dai ya rabu a kan wasu muhimman batutuwa: ko za a tsaga jihohi a sabon tsarin Tarayyar Nepal din ne a matakin kabilu ko kuma akasin haka.

Karin bayani