Sri Lanka ta ce Tamil ba su mamaye arewaci ba

Image caption masu zanga zanga a Sri Lanka

Ministan tsaron Sri Lanka dan rigima Gotabhaya Rajapaksa ya gayawa BBC cewar bai dace a cigaba da kallon arewacin kasar ba a matsayin yankin da 'yan kabilar Tamil su ka mamaye ba.

Ya kare yunkurin baya-bayan nan da aka yi na maye gurbin jami'an Tamil dake can da wasu daga tsibirin da 'yan sinhala suka fi rinjaye.

Yace, 'yan Sinhala da al'ummar Musulmi suna da 'yancin zama yankin a yanzu da aka daidaita al'amurra a yankin da aka gwabza fada.

Arewacin kasar ne dai babban sansanin 'yan tawayen Tamil a lokacin da ake yakin basasar da ya dauki shekaru ana gwabzawa.

Karin bayani