Shaidar kisan kiyashin da akai a Houla

Kofi Annan, wakilin MDD a Syria Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kofi Annan, wakilin MDD a Syria

An samu shaida ta farko daga garin Houla na kasar Syria, na wani da ya ce ya ga yadda aka halaka fiye da mutane dari a ranar juma'ar data gabata, a wani kisan da Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana a matsayin wani mummunan kisan gilla.

Daga cikin wadanda aka halaka har da kananan yara da dama lokacin da tankokin yaki suka yi ta luguden wuta a gidajen jama'a.

Wasu rahotanni dai sun ce wasu kananan yaran an yake musu makogoro ne, lamarin da yayi matukar girgiza kasashen duniya.

Wani faifen vidiyo da BBC bata tabbatar da sahihancinsa ba, ya nuna wani 'dan karamin yaro mai suna Ali Al Sin yana amsa tambayoyin da wani ke yi masa inda ya ke cewa:

"Na ga wasu tankokin yaki na zagayawa layi-layi, kusa da gidajenmu suna ta barin wuta, daga bisani sai naga tankokin yakin sun tsaya, inda wasu sojoji suka fito daga ciki suka yi ta harbi har sau biyar a 'kofar gidanmu."

Karin bayani