An kashe mutane uku a wani hari a Potiskum

boko haram
Image caption Ana zaman zullumi a jihar Yobe

Rahotanni daga birnin Potiskum a jihar Yobe sun ce mutum uku sun hallaka yayin da biyar suka sami raunuka a lokacin da wasu 'yan bindiga da ba a san ko su wanene ba suka kai hari a gidan wani babban malamin 'yan Shi'a.

Su dai mabiya mazhabar ta Shi'a na zargin jami'an tsaro ne da kai masu wanan harin na jiya, inda suka ce sun tsinci wasu harsasai da ke dauke da tambarin jami'an tsaro.

Sai dai rundunar 'yan sanda a jihar Yobe ta musanta wannan zargi.

A cewar su 'yan shi'ar suna rike da shaidar kwanson harsasai dake da tambarin jami'an tsaro.

Karin bayani