BBC navigation

Ma su zanga-zanga a Masar sun far wa ofishin Shafiq

An sabunta: 29 ga Mayu, 2012 - An wallafa a 07:59 GMT

Masu zanga-zanga a Masar

Ma su zanga-zanga a Misra, sun far wa babban ofishin kamfe na dan takarar shugaban kasa Ahmed Shafiq a babban birnin kasar Cairo.

Daruruwan masu zanga-zangar sun birkita ofishin kuma sun fasa gilasan tagogin ofishin gami da yage fastoci.

An dai cinna wa gidan wuta amma bata ci sosai ba.
Zanga-zangar ta zo ne wasu saoi kadan bayan da Hukumar zabe ta kasar ta bada sanarwar zabe zagaye na biyu tsakanin Mr Shafiq wanda tsohon Prime Minista ne a gwamnatin da ta shude ta Hosni Mubarak da kuma Mohammed Mursi na Muslim Brotherhood.

Nan da makwanni uku ne dai za ayi zaben zagaye na biyu.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.