Kofi Annan ya nuna damuwa akan Syria

Hakkin mallakar hoto AFP Getty

Wakilin Majalisar Dinkin Duniya kan rikicin kasar Syria Kofi Annan ya nuna damuwa akan irin kashe-kashen da ake yi a kasar

A wata ganawa da shugaba Bashar Al Assad, Mista Annan yace Syria na dab da fadawa cikin wani mummunan yanayi.

Mr Annan ya kuma ce shirin sa na wanzar da zaman lafiya a Syriar yana bukatar kwararan matakai domin kawo karshen tashin hankalin da ake yi a kasar.

Yanzu haka Kasashen Amurka da Burtaniya da Faransa da Jamus da Spain da Italiya hade da kasashen Australia da Canada duk su fara janye jakadun su daga Syria.

Ofishin Majalisar Dinkin Duniya dake kula da kare hakkin bil'adama, ya ce binciken daya gudanar kan kashe kashen da aka yi a garin Houla na kasar Syria, ya nuna cewa akasarin wadanda aka kashe an yi musu kisar gilla ne.

Wani kakakin Majalisar Dinkin Duniya ya ce masu sa ido na Majalisar wadanda yanzu haka suke kasar Syria, sun gano cewa kasa da mutane 20 ne aka harbe su da bindiga daga cikin mutane fiye da 100 da aka kashe.

Ya kara da cewa wasu shaidu sun zargi 'yan bindiga dake goyon bayan gwamnati ne da wannan danyen aiki, inda Majalisar ta ce kashe kashen musamman na 'kananan yara wani babban laifi ne da aka aikata akan bil'adama.

Karin bayani