Yawan futar da yaran riko na karuwa a Afrika

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Hedikwatar AU a Adis ababa

Yawan yara 'yan Afrika da iyaye daga wadansu nahiyoyin ke daukarsu don riko na cigaba da karuwa.

A cewar wani rahoto da za a fitar a yau, a Addis Ababa babban birnin kasar Habasha, a shekera ta 2010 , yara fiye da dubu shida ne aka dauka daga kasashen su domin riko a kasashen waje.

Ana cigaba da nuna damuwa akan halin da yaran kan tsinci kansu idan sun bar kasashensu domin fara sabuwar rayuwa da iyayen da suka dauke su riko.

Galibin irin wadannan yara dai na gidan marayu inda wasun su an mutu an bar su ne wasu kuma wadanda aka haifa aka jefar akan titi ko a kwararo ne.

Wasu lokutan irin wadannan yaran na shiga wata rayuwa bayan da suka samu iyayen riko.

Karin bayani