Mit Romney ya zama dan takarar Republican

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Obama da Romney

Tsohon gwamnan MassaChussetts Mitt Romney ya yi nasarar zama dan takara na Jam'iyyar Republican da zai kalubalanci Barrack Obama a zaben Shugaban kasa na Amurka da za a gudanar cikin watan Nuwamba.

Alkalumma sun nuna cewar ya cinye zaben fidda gwanin takara da aka yi a Jihar Texas inda ya samu kuri'un wakilan jam'iyyar dubu da dari daya da goma sha-hudu abinda ya tabbatar da zamansa dan takarar.

Mr Romney dai yana ta kamfe a Colorado da kuma Nevada a yau wasu garuruwa da ake tsammanin za a fafata a zaben.

Ra'ayin masu kada kuria na nuni cewa yan takarar na tafiya kafada da kafada a kamfe din da ake duba wanene zai fi inganta tattalin arziki.

Karin bayani