An samu asarar rayuka a jihar Cross River

wasu mayakan sa kai a yankin Niger Delta Hakkin mallakar hoto bbc
Image caption wasu mayakan sa kai a yankin Niger Delta

Mutane kusan talatin ne suka rasa rayukan su, sakamakon wani rikicin kan iyaka tsakanin wasu al'ummomi biyu, dake Jihar Kuros Riba da kuma Akwa Ibom, a kudu maso kudancin Najeriya.

Rahotanni dai na nuna cewa, akwai wasu mutanen da dama da suka samu raunuka, a dukkan bangarorin biyu , baya ga wasu da ake cewa sun bace.

Rahotanni na cewa an fille kan basaraken kauyen.

Yanzu haka mutane da dama na can na korafin rasa matsugunansu, sakamakon yadda suka ce an rushe dukkan gidajen kauyen.

Hukumomin 'yan sanda sun ce suna kokarin daukar matakan shawo kan wannan rikici wanda ake cewa karo na biyu kenan yana barkewa.

Karin bayani