BBC navigation

An hallaka mutane shida a Maiduguri

An sabunta: 30 ga Mayu, 2012 - An wallafa a 18:31 GMT
Jami'an tsaro na binciken ababen hawa a Maiduguri

Jami'an tsaro na binciken ababen hawa a Maiduguri

Rahotanni daga Maiduguri, babban birnin Jihar Borno da ke arewacin Najeriya, sun ce wadansu 'yan bindiga sun kai hari a kan wani gidan burodi inda suka hallaka wadansu ma'aikatan gidan, sannan suka jikkata wadansu.

Sai dai kuma ana samun rahotanni masu karo da juna dangane da adadin mutanen da suka rasa rayukansu a al'amarin, wanda ya faru a daren ranar Litinin.

Daya daga cikin shugabannin kungiyar masu gasa burodi a Jihar ta Borno ya shaidawa BBC cewa "mutum shida sun mutu—na gansu da ido na—mutum shida kuma suna asibiti".

Rundunar hadin gwiwa mai tabbatar da tsaro a birnin na Maiduguri ta tabbatar da faruwar wannan al'amari, amma kuma adadin da ta bayar na wadanda suka mutu ya saba da na kungiyar masu gasa burodin.

Kakakin rundunar, Laftanar Kanar Sagir Musa, ya ce da misalin karfe biyu na daren ranar Litinin din ne suka samu labarin cewa wadansu wadanda ba a san ko su wanene ba sun je gidan burodin, inda suka "kashe mutum biyu, kuma suka jikkata mutum biyu, sannan suka kwashi kudin da har yanzu ba a san ko nawa ba ne".

Birnin na Maiduguri da ma wadansu sassan Jihar ta Borno na ci gaba da fama da jerin hare-hare da kashe-kashe, al'amarin da ke dada jefa jama'a cikin zullumi, yayin da wadansu ke kauracewa zuwa wadansu jihohin.

A halin da ake ciki kuma, rundunar tsaron hadin gwiwa a Jihar Kano ta tabbatar da cewa ta kama wani wanda ake zargin dan kungiyar Jama'atu Ahlisunna Lidda'awati Wal Jihad ne.

Ko da yake rundunar ba ta yi wani karin bayani ba, wadansu kafofin yada labarai sun ruwaito cewa mutumin babba ne a kungiyar, wadda aka fi sani da suna Boko Haram.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.