Kofi Anan ya ce Syria ta kai mutane bango

Image caption Kofi Anan

Wakilin kasashen duniya ga kasar Syria Kofi Annan ya gaya wa Shugaba Assad cewa gwamnatinsa ta kai mutane iya wuya, sakamakon kisan farar hula fiye da dari daya da aka yi a garin Houla.

A tattaunawarsu a birnin Damascus, Mr Annan ya gaya wa Mr Assad cewar lallai ne ya dauki manyan matakai na aiwatar da sharudda shida da aka zayyana na cimma zaman lafiya.

Ya sake nanata cewar dole ne sojojin gwamnatin Syria da mayakan sa kai dake rufa mata baya su daina kai hare-hare.

Shugaba Francois Hallande na Faransa ya ce ba a yanke kauna ba ga daukar matakin soji don kare abinda ya kira kisan da Shugaba Bashar Al Assad yake yi wa mutanensa.

Karin bayani