An yanke wa Charles Taylor daurin shekaru 50

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Charles Taylor

Kotun duniya da ke birnin Hague ta yanke wa tsohon Shugaban Liberia Charles Taylor hukuncin daurin shekaru 50 a gidan yari bisa laifin ingiza yaki a Sierra Leone.

A watan da ya gabata ne aka sami Mr Taylor da laifin ruru wutar aikata laifukan yaki a lokacin yakin basasar kasar Sierra Leone.

Masu gabatar da kara sun nemi a yanke masa hukuncin shekaru 80, abinda masu kare shi suka ce yayi yawa matuka.

Mr Taylor din shi ne tsohon Shugaban kasa na farko da aka tuhuma a kotun duniya tun bayan kawo karshen yakin duniya na biyu.

Ana saran zai yi zaman gidan kaso a wani gidan yari da ke Burtaniya.

Karin bayani