Za a tisa keyar Assange zuwa Sweden

Julian Assange Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Julian Assange

Kotun Koli a London ta amince da a tisa keyar mutumin nan da ya kirkiro shafin Internet mai kwarmato bayanai na Wikileaks, watau Julian Assange, daga Birtaniya zuwa kasar Sweden inda ya ke fuskantar zargin yin lalata da wasu mata.

Alkalai biyar daga cikin bakwai na kotun sun yi watsi da karar da Mr Assange ya daukaka.

Lauyoyinsa sun gabatar da hujjar cewar bukatar ta gwamnatin Sweden ta saba ka'ida.

Magoya bayan Mr Assange dai na farbagar cewa, kasar Sweden na iya mika shi ga gwamnatin Amurka, domin gurfanar da shi a gaban kuliya bisa zargin wallafa bayanan sirri.

An dai jinkirta tisa keyar tasa da tsawo mako guda, inda ake ganin akwai yiwuwar za'a iya bashi izinin daukaka kara.