An kashe wani Bajamushe a Kano

Edgar Fritz Raupach Hakkin mallakar hoto x
Image caption Edgar Fritz Raupach

Rahotanni daga Najeriya sun ce an kashe wani Bajamushe da aka yi garkuwa da shi a cikin watan Janairun da ya gabata.

Rahotannin sun ce wadanda suka yi garkuwa da shi din ne suka hallaka shi a birnin Kano a lokacin da sojoji suka yi kokarin ceto shi.

Wakilin BBC ya ce wata majiyar tsaro ta ce an kashe Bajamushen ne da sanyin safiyar yau Alhamis, a lokacin da sojoji suka yi kokarin ceto shi, kuma wani likita ya ce ya ga gawarsa.

Wani kakakin rundunar sojin Najeriar ya ce wani gungun 'yan bindiga ne da ake zargi suna da alaka da reshen kungiyar al Qaeda a Arewacin Afrika, AQMI, suka kashe Edgar Fritz Raupach, wanda Injiniya ne.

Wasu rahotanni na cewa an kashe mutane kimaninbiyar dake garkuwa da dan kasar ta Jamus.

A halin da ake ciki kuma, an yi garkuwa da wani dan Italiya a jihar Kwara dake yankin tsakiyar Najeriyar.

'Yan sandan Najeriya dai sun ce suna farautar wadanda suka yi garkuwa da shi, tun ranar Litinin.